Yayin taron majalisar gudanarwar kasar da ya gudana jiya Laraba, karkashin jagorancin firayminista Li Keqiang, an kuma amince da daukar wani jerin sabbin matakai.
Li Keqiang ya ce manufar kulla kawance ita ce, samar da ingantaccen kiwon lafiya da zai isa ga kowa, musammam ma yankunan karkara.
Ya ce an cimma nasarar samar da inshorar lafiya a fadin kasar, da kuma inganta ayyukan asibitocin karkara, yana mai cewa nasarar na daga cikin wadanda ke gaba-gaba a duniya, inda ya ce abun da aka fi bukata a yanzu shi ne, samun kwararrun jami'an lafiya.
Yayin da mutane ke neman ingantaccen kiwon lafiya da karin kudin shiga, tabbatar da daidaito wajen rabon kudaden da aka ware na kiwon lafiya a kasar na da matukar wahala.
Har ila yau, shirin na inganta hadin gwiwa tsakanin asibitoci na da nufin cike gibin dake akwai wajen samar da kudade ga asbitoci a matakai daban-daban. (Fa'iza Mustapha)