in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron sa kaimi ga kiwon lafiya na duniya karo na 9
2016-11-25 10:57:01 cri
An kammala taron sa kaimi ga kiwon lafiya na duniya karo na 9 a jiya Alhamis a birnin Shanghai na kasar Sin, inda aka samu nasarori da dama. Mataimakiyar shugaban hukumar kiwon lafiya da kayyade haihuwa ta kasar Sin Cui Li, ta yi jawabi inda ta bayyana cewa, a wannan karo ne aka shigar da tunanin kiwon lafiya a cikin ajandar samun bunkasuwa mai dorewa, da maida shi a matsayin alkawarin gwamnatin kasa da kasa, wannan ne karon farko na shirin sa kaimi ga kiwon lafiya. Kana kasar Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa don bude sabon babi na kiwon lafiya na duniya, da tabbatar da lafiyar jama'ar dukkan kasashen duniya.

Cui Li ta bayyana cewa, mahalartar taron sun more fasahohi da nasarori na kasa da kasa da yankuna a fannin sa kaimi ga kiwon lafiya bisa taken taron wato "kiwon lafiya yayin da ake kokarin samun bunkasuwa mai dorewa", kana sun yi mu'amala, da koyi da juna a wannan fanni, da cimma daidaito kan ayyuka da dama.

Babbar direktar hukumar kiwon lafiya ta duniya Margaret Chan, ta bukaci mahalarta taron da su yi kyakkyawan amfani da wannan damar don sa kaimi ga fannin kiwon lafiya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China