in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran tsawon rayuwar al'ummar lardin Guangdong na Sin zai kai shekaru 77.8 a 2020
2017-03-20 09:48:06 cri

Wani rahoton kiwon lafiyar na kasar Sin ya ruwaito cewa, ana sa ran matsakaicin mizanin tsawon rayuwar al'ummar lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin zai kai shekaru 77.8 a shekarar 2020, sakamakon ingantuwar tsarin kiwon lafiya.

A cewar rahoton kiwon lafiya da lardin ya fitarwa bisa shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 13 na kasar Sin wato daga 2016 zuwa 2020 a baya-bayan nan, matsakaicin mizanin tsawon rayuwa ya karu zuwa shekaru 77.1 a shekarar 2015, wanda ya dara na shekarar 2015 da shekara guda, ya kuma ya zarce na kasar baki daya da 0.8.

An kuma samu raguwar adadin mace-macen mata masu juna biyu da kashi 11.56 cikin mata 100,000 a shekarar 2015, adadin da ya ragu da kashi 12 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2010.

Haka kuma, an samu raguwar mutuwar jarirai da kashi 2.64 cikin jarirai 1,000 a shekarar 2015, adadin da ya ragu da kashi 45.3 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2010.

Shirin na shekaru biyar biyar na 13 ya bayyana cewa, lardin zai inganta ayyukansa a fannin yaki da cututtuka masu yaduwa, samar da kayayyakin motsa jiki ga al'umma, da kuma fadada tsarin inshore, ta yadda zai isa ga kowa. (Fa'iza Mustapha.)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China