Mahukuntan kasar Sin sun lashi takwabin gyara tsarin albashin ma'aikatan lafiya na kasar, a wani mataki na samarwa 'yan kasar ingantacciyar tsarin kiwon lafiya.
Babban ofishin kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar mai kula da nasarorin da aka cimma a fannin yin gyare-gyare a bangaren kiwon lafiyar kasar ne suka gabatar da wannan shawara.
Manufar daukar wannan mataki, a cewarsu ita ce, karfafa gwiwar ma'aikatan lafiyar, ta yadda za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Bugu da kari takardar shawarar ta bayyana cewa, za a bullo da tsarin da jama'a za su rika tantance kwazon ma'aikatan lafiyar, matakin da zai iya kai su ga samun karin albashi.(Ibrahim)