Rahotanni sun bayyana cewa tsarin na shekaru 10, ya kunshi shirin kasar na kariya, tare da magance cututtukan da ke da wahalar magani, ko masu dadewa ana faman jiyyar su, kamar ciwon daji, da na zuciya da Sukari da dai sauran su.
Tsarin wanda aka fitar a Talatar nan, zai maida hankali ne ga kyautata lafiyar al'umma, da rage yiwuwar kamuwa da wadannan nau'o'i na cututtuka tsakanin al'ummun dake cikin hadarin kamuwa da su, tare da daukar matakan inganta lafiyar wadanda suka riga suka kamu da su.
Har wa yau tsarin na kunshe da wasu muhimman sassan 8, da suka kunshi sashen ilmantarwa, da inganta matsayin gwaji da jinya, da inshorar lafiya da ma dabarun bada tallafi ga majiyyata. (Saminu Hassan)