Kasar Sin na fatan wata bunkasuwa cikin sauri a bangaren kiwon lafiya kafin shekarar 2020, duk tare da karfafa karfin kawo kirkire kirikire na bangaren, da kuma kara ingancin kayayyaki, a cewar wani shirin da aka fitar a ranar Litinin.
Adadin kudin shiga da za a samu a bangaren a ko wace shekara zai haura fiye da kashi 10 cikin 100, in ji ma'aikatar masana'antu da fasahohin sadarwa ta kasar Sin a kan shafinta na yanar gizo.
Kuma wajibi ne kamfanonin likitanci za su ci gaba da kara zuba jari a cikin ayyukan bincike da na ci gaba, har zai kai fiye da kashi 2 cikin 100 na kudaden shigarsu a jimilce nan da shekarar 2020, a cewar wannan shiri.
Kasar Sin za ta kafa cibiyoyin kirkire kirkire domin kera kayayyakin likitanci, tare da wani zuba jarin da zai fito daga gwamnati da bangarori masu zaman kansu. (Maman Ada)