Yau Jumma'a ranar 10 ga wata, kotun kundin tsarin mulkin kasar Koriya ta Kudu, ta sanar da amincewa da kudurin tsige Park Geun-hye daga mukaminta na shugabar kasar, lamarin da ya sa Park Geun-hye ta zama shugaba ta farko da aka tsige ta daga mukamin shugaban kasa a tarihin kasar Koriya ta Kudu.
Bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar, za a raba Park Geun-hye daga mukamin shugabar kasar, kuma za a cire ikonta na samun kariya daga gurfana gaban kuliya domin fuskantar shari'a. Bugu da kari, dole ne a shirya babban zabe na kasar cikin kwanaki 60 masu zuwa.(Kande Gao)