in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi zanga-zanga a Koriya ta Kudu domin sauke shugabar kasar daga mukaminta
2016-10-30 13:21:52 cri
An yi babban taron gangamin al'umma a Seoul, babban birnin kasar Koriya ta Kudu, a ran 29 ga wata, domin korar shugabar kasar Park Geun-hye daga mukaminta, bisa zargin da aka yi mata cewa, abokiyarta ta sa hannu cikin harkokin kasa.

Jiya Asabar da dare, wasu kungiyoyin fararen hula sun yi gangami a dandalin Cheong gye cheon dake birnin Seoul, kuma bisa labarin da aka samu, an ce, wanda ya shirya gangamin ya bayyana cewa, mutane kimanin dubu 20 ne suka halarci gangamin, amma bisa kididdigar da rundunar sojan kasar ta yi, adadin mutanen da suka halarci gangamin bai wuce dubu 9 ba.

Bugu da kari, mutanen da suka halarci gangamin sun kara yin ihun a kori shugabar kasar daga mukaminta, har ma suka nemi zuwa fadar shugabar kasar ta Blue House, amma 'yan sanda suka hana su.

Shugaban gangamin ya ce, za a kira wani gangamin da zai fi wannan girma a ranar 12 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Baya ga birnin Seoul, an gudanar da irin wannan taron gangami a birane daban daban na kasar Koriya ta Kudu a jiya, cikin har da Busan, Ulsan, Kwang Ju da dai sauransu.

Kana, bisa binciken da aka yi a makon nan, adadin masu goyon bayan gwamnatin dake karkashin jagorancin shugabar kasar Park Geun-hye ya ragu zuwa kashi 17 bisa dari, wanda ya kasance mafi karami bayan ta hau kan ragamar mulkin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China