in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna yabo ga taron shugabannin kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu
2015-11-02 11:02:24 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yaba da taron da shugabannin kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu suka gudanar a birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu, kana ya yi fatan taron zai karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen uku da sa kaimi ga samun zaman lafiya da wadata a yankin arewa maso gabashin nahiyar Asiya.

Mr Ban Ki-moon wanda ya bayyana hakan cikin sanarwa da ya bayar ya kuma yaba da ganawar da firaministan kasar Sin Li Keqiang, da shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye, da firaministan kasar Japan Shinzo Abe suka yi. Yana fatan shugabannin kasashen uku za su sake yin shawarwari don inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen uku har ma da dukkan yankin arewa maso gabashin Asiya. Ya ce MDD na fatan dukkan kasashen dake yankin za su hada kai tare da imani da juna ta yadda za su hada kai wajen samar da zaman lafiya da wadata a yankin baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China