A wannan rana, shugabannin manyan jam'iyyun adawa uku na kasar sun halarci wannan taron gangamin.
A labarin da aka bayar, ban da birnin Seoul, al'ummar kasar da ke biranen Busan da Jeju da sauransu ma sun yi zanga-zanga ko gangami don bukatar shugabar ta yi murabus.
Manazarta suna ganin cewa, babban taron gangami da aka gudanar a wannan rana ya sake bayyana rashin jin dadin al'umma ga gwamnatin Park Geunhye.
A binciken da Gallup Korea ya gudanar, an ce, a cikin watan nan na Nuwanba, yawan goyon bayan da aka nuna wa shugaba Park Geunhye ya kai kimanin kashi 5% kawai a cikin makwanni biyu a jere, adadin da ya kai wani matsayi mafi kankanta a tarihin shugabannin kasar.(Lubabatu)