in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koriya ta Kudu: Dubu-duban jama'a sun yi gangami domin bukatar shugabar kasar ta yi murabus
2016-11-06 12:44:02 cri

Ranar 5 ga wata, dubu-duban jama'ar kasar Koriya ta Kudu sun yi gangami a tsakiyar birnin Seoul, hedkwatar kasar domin nuna adawa da yadda kawar shugabar kasar madam Park Geun-hye ta tsoma baki a cikin harkokin kasa, tare da bukatar shugabar kasar da ta yi murabus daga mukaminta. Masu shirya gangamin sun ce, mutane kimanin dubu 200 ne suka shiga gangamin, amma kafofin yada labarun kasar sun ruwaito kalamin 'yan sandan wurin na cewa, mutane kimanin dubu 45 sun shiga gangamin a hakika.

A wannan rana kuma, baya ga Seoul, al'ummar kasar da ke a biranen Kwangju, Daegu, Busan, Jeju da ma sauran wasu wuraren kasar sun yi zanga-zangar nuna adawa da shugabarsu.

Ranar 25 ga watan jiya, madam Park Geun-hye ta roki gafarar jama'ar kasar dangane da yadda abokiyar arzikinta ta tsoma baki cikin harkokin kasar. A ranar 4 ga watan nan kuma ta sake rokon gafara dangane da lamarin, tare da kuma amincewa da a gudanar da bincike kan lamarin.

Amma duk da haka abubuwan da madam Park Geun-hye ta yi ba su taimaka wajen kawar da shakku da kin yarda da ake nuna mata ba. Reshen kamfanin Gallup a kasar Koriya ta Kudu ya fitar da sakamakon binciken jin ra'ayoyin jama'a a ranar 4 ga wata, inda a cewarsa, a makon farko na watan Nuwamban bana, yawan 'yan Koriya ta Kudu dake goyon bayan madam Park Geun-hye ya kai kashi 5 cikin dari kawai bisa jimillar jama'ar kasar, adadin da ya kasance mafi kankanta a cikin tarihin shugabannin kasar Koriya ta Kudu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China