Kakakin fadar shugaba ta kasar Cheong Wa Dae, Jung Youn-kuk ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a wannan rana cewa, shugaba Park Geun-hye ta fahimci matukar mummunan yanayin da ake ciki a yanzu, kuma ta tsaida wannan kuduri ne domin biyan bukatun bangarori daban daban. Amma, bisa la'akari da muhimmancin gudanar da harkokin kasa yadda ya kamata, ba ta amince da takardun murabus na wasu jami'ai ba.
Manazarta na ganin cewa, shugabar ta yiwa gwamnatin ta garanbawul ne, gabanin zabo wasu mutanen da suke mafiya dacewa da wasu mukamai. Hakan ya kuma nuna cewa, matsin lambar da kafofin watsa labaru suka yi, da burin kwantar da hankalin jama'a da take dauka da muhimmancin gaske sun sanya ta daukar matakin.
A ranar 25 ga watan nan ne dai shugaba Park Geun-hye, ta nemi gafara daga al'ummar kasar ta, sakamakon fayyace wasu takardun da Choi Soon-sil, wata mai goyon bayanta ta yi. Sai dai har ya zuwa yanzu ana faman daukar kwantar da kurar da wancan lamari ya tayar.
A ranar 29 ga watan nan, wasu gungun 'yan kasar sun yi zanga-zanga a cibiyar birnin Soule, suna masu bukatar Choi Soon-sile ta yi murabus daga mukaminta. (Bilkisu)