A jiya Laraba ne karamin ministan ma'aikatar hakar ma'adanai na kasar Rwanda, ya bayyana a gaban babbar kotun Nyarugenge dake Kigali, inda ake tuhumarsa da laifin nuna fifiko da sauya wasu takardun aiki.
Ana tuhumar tsohon minista Evode Imena da aka tsare a watan Janairun da ya gabata bayan an sallame shi daga aiki, tare da wasu tsoffin jami'an gwamnati biyu da suka yi aiki a tsohuwar ma'aikatar kula da albarkatun kasa ta Rwanda.
Lauya mai shigar da kara na zargin mutanen uku da gaggauta yiwa wani kamfani rajista ba bisa ka'ida ba, inda aka ba shi lasisin hakar ma'adanai a yankin Nduba, dake wajen birnin Kigali.
A cewar lauyan, daga bisani, kamfanin mai suna JDJ ya sayar da hakkokinsa ga wani kamfani mai suna KNM a kan kudi dalar Amurka dubu ashirin da amincewar Ministan. ( Fa'iza Mustapha)