Addu'ar ta shekara shekara, wanda kungiyar zumuncin shugabannin Rwanda ta shirya. Ya samu halartar manyan shugabanni a kasar, domin yiwa kasar addu'o'i da kuma yiwa jagororin kasar addu'a.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya ce shekarar 2016 da ta gabta shekara ce mai kyau ta fuskar cigaban da kasar Rwanda ta kuduri aniyar yi, duk da cewar akwai abubuwan da ba'a kammala ba.
Ya ce ya zama dole a yiwa Allah godiya kana a godewa mutanen kasar saboda irin nasarorin da aka cimma a shekarar ta 2016, kuma ana fatan samun alkhairai a cikin sabuwar shekarar 2017.
Kagame ya ce an cimma nasarori masu yawa a shekarar 2016, kuma ana fatan cigaba da dorawa daga inda aka tsaya domin samun makoma mai kyau ga kasar.
Ya kuma bukaci alummar kasar ta Rwanda da su zage damtse don yi aiki tare domin cimma muradan da aka sa a gaba.
Sannan ya bukaci matasan kasar da su yi amfani da babbar damarsu domin kasar ta cimma nasarori masu yawa a nan gaba. (Ahmad)