Rahotan wanda aka wallafa jiya a birnin Davos na kasar Switzerland, ya yi amfani da alkaluman yadda kasa ta bunkasa, da yadda ta ke janyo da kuma rike kwararrunta, yadda ta ke taimakawa masananta da matakan da za su bunkasa kwarewarsu ta yin takara.
GTCI dai ta gudanar da bincikenta ne a kan kasashe 118, inda ta yi bitar tasirin canje-canjen fasahar zamani a fannin kwarewar gogayya. Kuma kasar Rwanda ce ta 6 inda kwararru suka fi yin takara a kasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar Sahara, kana kasa ta 91 a duniya a wannan fannin inda ta samu kaso 36.76 cikin 100
Kasar Mauritius ce ta ke kan gaba a kasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar Sahara, sai kasashen Botswana da Afirka ta kudu da ke biye da ita.(Ibrahim)