Ta wannan muhimmin biki, an nuna kaddamar da hanyar zirga zirgar jiragen sama dake hada a halin manyan hedkwatocin kasashen biyu, in ji darekta janar na kamfanin RwandAir, Jean Paul Nyirubutama.
A halin yanzu, ya cigaba da cewa, kamfanin zirga zirgar jiragen sama na kasa, wato RwandAir, zai rika zuwa Cotonou, wanda a ganinsa, ita hedkwatar tattalin arziki ta yammacin Afrika, sau uku ciki mako tare da yada zango a birnin Douala na kasar Kamaru da kuma birnin Libreville na kasar Gabon
Mista Nyirubutama, ya nuna cewa, wannan zirga zirgar jiragen sama zata taimakawa wajen kai da kawo tsakanin Cotonou da Kigali ba tare da wata matsala ba, kuma hakan na tabbatar da gajiyar yarjejeniyar dangantaka kan ayyukan sufurin sama da kasashen biyu suka rattaba hannu a ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata, domin karfafa cudanya tsakanin al'ummomin Benin da Rwanda da kuma bunkasa musanyar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
A cewar wasu majiyoyin diflomasiyya a birnin Cotonou, dangantaka tsakanin Benin da Rwanda na shafar fannoni da dama, musammun ma kasuwanci da bunkasa zuba jari, musanyar kwararru, yawon bude ido, saukaka shige da ficen dukiyoyi da jam'a, sufurin jiragen sama tsakanin Kigali da Cotonou da masana'antun saka. (Maman Ada)