Kwamitin kasa domin yaki da kisan kare dangi (CNLG), ya gabatar takardar mai kunshe da bayanai na hafsoshin rundunar sojojin Faransa a ranar Litinin, bayan matakin sake bude bincike da kasar Faransa ta yi kan harbo wani jirgin saman dake dauke da shugaban kasa na lokacin, Juvenal Habyarimana, lamarin da ake gani shi ne dalilin da ya janyo kisan kare dangi.
Fitar da wadannan sunaye zai kara lalata dangantaka da tuni take tsami tsakanin Rwanda da Faransa, a cewar masu nazarin harkokin duniya.
A cikin wani rahoto dake kunshe da cikakken bayani da aka fitar a ranar Litinin, CNLG ta bayyana cewa hafsoshin Faransa da aka ambato suna da hannu a kasar Rwanda a lokacin kisan kare dangi kana sun halarci kai tsaye ga kisan mutane.
Jean Damascene Bizimana, sakataren zartaswa na CNLG, ya bayyana cewa kwamitin ya gabatar da wannan kundi bayan boye gaskiya karara kan matsayin Faransa a cikin kisan kare dangi.
Binciken abubuwan da suka faru ya nuna cewa hafsoshin Faransa da 'yan siyasa sun tafka manyan laifuffukan gaske a Rwanda, in ji jami'in a cikin wata sanarwa da aka mikawa 'yan jarida. (Maman Ada)