Shugaba Kagame ya yi wannan kiran jiya Litinin a lokacin da yake jawabi a gaban tawagar da ke halartar taron kolin kungiyar tarayyar Afirka (AU) da ya gudana a birnin Kigali, fadar mulkin kasar ta Rwanda.
Kagame ya ce, amfani da tsarin sadarwa na bai daya zai taimakawa al'ummomin nahiyar buga waya cikin sauki da kuma rahusa. Ya ce, wannan matakin farko ne na kokarin da ake na samar da kasuwar bai daya ga kasashen nahiyar.
Shugabannin kasashen Rwanda da Gabon ne dai suka kaddamar da tsarin sadarwar, a wani mataki na soke kudaden buga waya da aka caja a wajen kasashen na Afirka tsakanin wadannan kasashe biyu. Ana kuma fatan wannan mataki zai taimaka wajen rage kudaden buga wayar da ake caja.
Shugaba Kagame ya ce bai ga dalilin da zai sa al'ummar Afirka za su rika biyan irin wadannan kudaden buga waya yayin da suke wata kasa a cikin nahiyarsu ba. (Ibrahim)