Tawagar na kunshe da mambobi tara da suka fito daga majalisar shiyyar wadda ta ziyarci a ranar Talata dandamalin tunanin kisan kare dangi bisa tsarin tawagarta ta bincike kan akidar kisan kare dangi a gabashin Afrika. Gaban 'yan jarida jam kadan bayan ziyararta a cibiyar, Judith Pereno, mambar Kenya na ALEA, ta bayyana cewa akidar kisan kare dangi wata akida ce da bai kamata masu fada ajin siyasa na shiyyar su watsi da ita ba.
Ana da watannin uku domin kara sani kan akida da karyata kisan kare dangi daga cikin al'ummomin shiyyar. Kasar Rwanda ita ce misalin nazari na wannan batu bisa dalilin kisan kare dangi na shekarar 1994, in ji madam Pereno.
Ra'ayi na irin wannan bincike ya biyo bayan wani kuduri mai zurfi na dan majalisan Kenya Abubakar Ogle da kuma majalisar ta amince da shi a farkon shekarar da ta gabata dake yin allawadai da kisan kare dangi, akidarsa da karyata shi. 'Yan majalisan sun yi niyyar shirya wani bincike domin kimanta girman akidar kisan kare dangi da karyata shi a cikin kasashe mambobi. (Maman Ada)