Hua ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sao Tome and Principe ta bayar da sanarwa a jiya Talata cewa, ta tsai da kudurin yanke dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da yankin Taiwan, Sin ta nuna yabo ga kudurin, da yin maraba da matakin da kasar ta dauka na bin ka'idar Sin daya tak.
Hua ta kara da cewa, a halin yanzu, tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak ya dace da yanayin kasa da kasa da burin jama'a. Sin tana son raya dangantakar hadin gwiwa da sada zumunta a tsakaninta da sauran kasashen duniya bisa tushen ka'idoji biyar na zaman tare cikin lumana da ka'idar Sin daya tak. (Zainab)