Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, yankin Taiwan wani kashi daya ne na kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin halaliyyar gwamnati ce dake wakilci kasar Sin baki daya, wadda kuma kasa da kasa sun amince da ita.
Ka'idar Sin daya tak tushen siyasa ne yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, Sin ta kalubalanci hukumomin kasar Amurka da abin ya shafa da su bi manufar Sin daya tak, da cika alkawarin ka'idojin hadaddiyar sanarwa na Sin da Amurka guda uku, da warware batun yankin Taiwan yadda ya kamata don magance matsalolin dake kawo illa ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)