A yau kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya yaba wa Mr. Ayrault dangane da goyon bayan manufar "kasar Sin daya tak a duniya".
Ban da wannan kuma, manyan jami'an kasashen Jamus da Australia da dai sauransu sun bayyana aniyarsu ta kare manufar "kasar Sin daya tak a duniya". Dangane da wannan lamari, Geng Shuang ya bayyana cewa, tabbatar da manufar "kasar Sin daya tak a duniya" shi ne muhimmin tushen raya dangantarkar abokantaka a tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya. (Maryam)