Ministan harkokin waje na kasar Sin ya yi sharhi a kan tattaunawar da Donald Trump ya yi tare da jagorar yankin Taiwan
A game da labarin tattaunawa ta wayar tarho da zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi tare da shugabar yankin Taiwan Tsai Ing-wen, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi a jiya Asabar ya bayyana cewa, wannan wani makirci ne na bangaren Taiwan, wanda ko kadan ba zai iya canza yanayin da ake ciki a duniya na kasancewar Sin, kasa daya tak a duniya.
Ministan ya kara da cewa, "A ganina, wannan ma ba zai iya canza manufar da gwamnatin kasar Amurka ta dade take dauka kan kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, manufar da ta zama tushe na bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu, kuma ba ma so a lalata wannan tushe na siyasa."