Makircin mahukuntan Taiwan ba zai iya sauya matsayin yankin na wani bangaren na kasar Sin ba
A game da tattaunawa ta waya da zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi tare da shugabar yankin Taiwan Tsai Ing-wen, kakakin ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, An Fengshan ya bayyana a jiya Asabar cewa, makircin mahukuntan Taiwan ba zai iya sauya matsayin yankin na wani bangare na kasar Sin ba, haka kuma ba zai canza yadda akasarin kasashen duniya ke daukar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya ba. Muna tsayawa tsayin daka a kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya tare da nuna rashin amincewa da ballewar Taiwan daga kasar Sin, muna da niyyar dakile nau'o'in ayyuka na jawo ballewar Taiwan, tare da sa kaimin dunkulewar kasar Sin.(Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku