Kafin haka, majalisar dokokin Amurka ta zartas da wata dokar da ta shafi aikin tsaron kasar, wadda a cikinta aka bayyana yunkurin karfafa mu'amalar jami'an Amurka da na Taiwan ta fuskar aikin soja. Dangane da wannan lamari, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, batun Taiwan ya shafi ikon mulkin kasa da cikakken yankin kasar Sin ne, don haka yana da muhimmanci matuka.
Jami'in ya kara da cewa, tun lokacin da majalisar dokokin Amurka ta fara tattaunawa kan kudurin dokar, kasar Sin ta sha nuna kin amincewarta a lokuta da dama kan wannan batu. Yanzu kasar Sin tana kalubalantar kasar Amurka da ta tsaya kan iya yarjejeniyoyin da ta kulla da kasar Sin, sa'an nan ta yi taka-tsantsan wajen tsoma baki kan batun Taiwan. Bai kamata ba a haifar da matsala ga al'amuran siyasar duniya, da raunata huldar dake tsakanin Sin da Amurka, in ji jami'in na kasar Sin.(Bello Wang)