Wang Yi, ya fadi haka ne yayin da yake zantawa da wakilin CRI a birnin Colombo, babban birnin kasar Sri Lanka jiyaAsabar. Wang ya kuma kara da cewa,
"Muna da dalili da kuma hakki wajen shakkar ainihin makarkashiyar wannan batun. Mun bukaci Amurka da ta dakatar da kiyaye tsaron kanta ta hanyar tada hankalunan sauran kasashe, balle ma lalata muradun tsaron sauran kasashe bisa hujjar kawo barazana ta fuska tsaro. Haka kuma muna fatan abokan kasar Koriya ta Kudu za su iya yin la'akari sosai kan cewa, ko aikin jibge tsarin Thaad zai iya ba da taimako wajen kiyaye tsaron kasarku ko a'a, ko zai iya ba da kyakkyawan tasiri wajen tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya ko a'a, ko zai iya taimakawa wajen warware batun nukiliya na zirin ko a'a. Dole ne bangarorin da abin ya shafa su yi taka tsantsan kan batun, kada su yi babban kuskure." (Kande Gao)