Sin ta kalubalanci Amurka da Koriya ta Kudu su dakatar da shirinsu na girke na'urorin kakkabo makama masu linzami na THAAD
A yau safe ne ma'aikatar tsaron kasar Koriya ta Kudu ta sanar da cewa, kasarta da kasar Amurka sun amince su girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami sanfurin THAAD a kasar Koriya ta Kudu. Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayar da sanarwar nuna rashin amincewa game da wannan batu. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana a nan birnin Beijing cewa, girke wadannan na'urori ba zai taimaka wajen cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya da kuma kiyaye zaman lafiya a zirin ba, sai ma ya kara kawo illa ga moriyar kasashen dake yankin ciki har da kasar Sin. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku