Haka kuma, bayan ganawarsa da shugaban kasar Mozambique Felipe Jacinto Newsy a babban birnin kasar, Maputo a ran 26 ga wata, Mr. Kamau ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su kara samar da taimakon jin kai ga wadanda suke fama da matsalar a kasar.
Bugu da kari, ya ce, a farkon shekarar bana, gamayyar kasa da kasa sun yi alkawarin samar wa kasashen Afirka dake fama da matsalar El Nio taimakon abinci, amma ya zuwa yanzu, kimanin kashi 50 bisa dari na alkawarin da aka yi ne kawai aka bayar. (Maryam)