A jiya Laraba ne dai shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na Mozambique, Filipe Jacinto Nyusi, inda suka yi musayar ra'ayi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da harkokin shiyya shiyya da na duniya da suka fi jawo hankulansu.
Cikin kalaman sa shugaban na Mozambique ya bayyana cewa, kasar sa na nuna goyon baya ga ra'ayin Sin na daidaita batun yankuna mallakar kasar, da batun yankin teku ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, bisa kuma yarjejeniyar da bangarorin da batun ya shafa suka daddale, da matsayar da suka cimma.
A kwanan baya kuma, gwamnatin Burundi ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su daidaita batutuwan ta hanyar shawarwari cikin lumana, bisa sanarwar ayyukan bangarori daban daban dake daf da tekun kudun. Ta kuma jaddada cewa kamata ya yi kasa da kasa su girmama kasashe masu ikon kansu game da 'yancinsu na zaben hanyar daidaita gardama. (Fatima)