Yayin ganawar ta su, Wang Yi ya ce yayin da Mozambique ke fafutukar samun 'yancin kai, Sin tana tsayawa haikan wajen nuna mata goyon baya, a halin yanzu, yayin da kasar ke kokarin samun wadata, kasar Sin ita ma za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da Mozambique. Ya ce bana shekara ce ta farko, ta fara aiwatar da shirin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannoni 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, a yayin taron kolin tattaunawar hadin gwiwa na Sin da Afrika wato FOCAC, wanda ya gudana a birnin Johannesburg. Kaza lika Sin na sa ran tattauna hadin gwiwa da kasar Mozambique karkashin inuwar shirin a karon farko, don taimakawa kasar samun ci gaba, da kawo moriya ga jama'ar ta.
Ya kara da cewa, bangarorin biyu za su iya inganta hadin gwiwa a fannonin masana'antu, da samar da fasahohin da Sin ta samu wajen raya masana'antu a Mozambique, da tattaunawa game da kafa unguwar masana'antu, da yankin raya tattalin arziki na musamman, da fitar da fasahohin zamani ga kasar, kana za su iya inganta hadin gwiwa a fannin gona. Kana Sin za ta kara horar da kwararru, da inganta hadin gwiwa da kasar wajen aikin samar da zaman lafiya da tsaro, don daukaka kwarewar Mozambique wajen tsaron kai, da samar da zaman lafiya.
Ban da wannan kuma, kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa da Mozambique wajen kawar da talauci, da inganta ilmi da kiwon lafiya da sauransu, don sa kaimi ga kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar. A karshe, kasashen biyu za su inganta shawarwari game da batun sauyin yanayi, da samun ci gaba cikin dogon lokaci, da sauran batutuwan duniya da na shiyya-shiyya, don tabbatar da moriyar kasashe masu tasowa.
A nasa bangare, Mr. Baloi ya ce ko a lokacin da Mozambique take kokarin neman 'yancin kanta, ko kuma a lokacin ta ke yunkurin raya kasar, Mozambique da Sin sun nuna wa juna goyon baya. Har wa yau Mozambique ta yi na'am da kasar Sin a fannin inganta hadin gwiwa da kasar a bangaren makamashi, da muhimman ababen more rayuwa, da kere-kere, da aikin gona, da sauransu, don kyautata hadin gwiwar samun moriyar juna. Mozambique ta jinjina sakamakon taron kolin na FOCAC na johannesburg, kuma tana fatan hadin gwiwa da kasar Sin, don samun ci gaba tare.(Bako)