Mr. Nkaissery ya yi watsi da zargin da wasu kafofin watsa labaran kasar ke yadawa ne a jiya Talata, yayin wani taron 'yan jaridu, yana mai cewa kafofin na yada wannan bayanai ne da wata mummunar manufa.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da wata jaridar kasar ta fidda wani rahoto dake cewa tsakanin watan Janairu zuwa Agustan bana, 'yan sandan kasar ta Kenya sun hallaka fararen hula 121. Kaza lika daga shekarar bara zuwa yanzu, 'yan sandan sun kashe mutane da yawan su ya kai 262 ba tare da gurfanar da su a gaban kuliya ba.
Mr. Nkaissery ya kara da cewa, a matsayin kasa mai bin doka da oda, babu yadda za a yi 'yan sandan Kenya su rika hallaka mutane ba tare da wani dalili na shari'a ba. Ya ce wannan alkaluma da jaridar ta fitar, ba za su tabbatar da zargin da ake yiwa 'yan sandan kasar na aikata kisan gilla ba.(Saminu Alhassan)