Labarin ya ce, yanzu jihohi 23 na Kenya suna fama da bala'in fari.
A daren ranar Jumma'a 14 ga wata, ministan raba iko da tsara shiri na Kenya Mwangi Kiunjuri ya bayyana wa kafofin yada labarai a birnin Nairobi, hedkwatar kasar cewa, kawo yanzu babu rahoto dangane da mutuwar mutane sakamakon karancin abinci. Ya ce, gwamnatin kasar ta dauki alkawarin cewa, tana kokarin shawo kan matsalar cikin gaggawa, za ta ba da agaji ga wadanda suke cikin tsananin bukata cikin lokaci.
Minista Mwangi Kiunjuri ya bayyana cewa, yanayin karancin abinci ya sami kyautatuwa sosai a shekarar bana, idan aka kwatanta bisa ga barazanar da aka fuskanta a bara inda mutane miliyan 2.5 ne suka yi fama da karancin abinci.(Fatima)