in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Kenya sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da 'yan ta'adda
2016-10-12 10:02:36 cri

'Yan sandan kasar Kenya sun cafke a ranar Talata a birnin Nairobi, hedkwatar kasar wani dan asalin kasar Burtaniya da wasu mata biyu 'yan asalin kasar Somaliya da ake zarginsu da kasancewa masu horar da kuma neman wa kungiyar Al-Shebab mayaka.

An kai wani babban samame a gidan dan asalin Burtaniyan dake Nairobi, wanda aka tantance sunansa da Tom, kuma an kama wadannan mata biyu tare da shi.

'Yan sandan sun gano wasu abubuwan dake tabbatar da zargin da ake musu da suka hada da takardun ba da horo, littattafai, rigunan kariya da kwamfutoci a yayin samamen da aka kai a gidan na dan Burtaniyan, wai shi Tom. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China