in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi bikin cika shekaru 22 da kawo karshen kisan kiyashi a Rwanda
2016-04-08 10:56:42 cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU a jiya Alhamis ta gudanar da bikin cika shekaru 22 da kawo karshen kisan kare dangi a kasar Rwanda. Bikin an gudanar da shi ne a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

A cewar AU, makasudin shirya bikin shi ne, domin zaburar da al'ummomin nahiyar Afrika da sauran kasashen duniya, wajen martaba rayuwar bil Adama, da kuma hadin gwiwa don tattabar da kare hakkin dan Adam a duniya.

Yayin bikin, an kunna kendira, sannan malaman addinai sun gudanar da addu'o'i, da rera wakoki da nuna wasannin kwaikwayo.

Aisha Abdullahi, kwamishiniyar AU ta sashen al'amuran siyasa, ta bukaci a dauki matakai na yakar dabi'ar kisan kiyashi a tsakanin al'umma.

Hope Tumukunde Gasatura, jakadar Rwandan a Habasha kuma zaunanniyar wakiliyar Rwanda a kungiyar AU ta ce, ana gudanar da bikin ne a ko wace shekara, domin fatar kada wannan ibtila'i ya maimaita kansa a kasar Rwanda da ma sauran sassa na duniya.

Rikici ya kaure ne tsakanin kabilar Tutsis da Hutu, bayan harbo jirgin sama dake dauke da tsohon shugaban kasar Rwanda Juvenal Habyarimana dan kabilar Hutu a rana 6 ga watan Aprilun shekarar 1994, inda 'yan kabilar Hutu suka zargi Tutsis da harbo jirgin, lamarin da ya haddasa mutuwar al'ummar kasar Rwanda sama da miliyan guda.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China