Rwanda dai a makon da ta gabata ta sanar da cewar bada dadewa ba zata fara kaurar da 'yan gudun hijiran kasar Burundi zuwa wassu kasashe domin kauce ma abinda ka iya faruwa sakamakon zama kusa da kasar su na haihuwa cikin lokaci mai tsayi.
Da yake hira da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin , Xinhua, Jean Philbert Nzabandora, wani dan shekaru 48 kuma daya daga cikin dubban 'yan gudun hijiran na Burundi dake zaune a sansanin 'yan gudun hijira na Mahama a gundumar Bugesera, kudancin kasar ta Rwanda yace suna cikin tsaro da kwanciyar hankali na cigaba da zama a Rwanda maimakon sake tsugunar da su a wasu kasashen da ba kwanciyar hankali.
Ya ce idan har za'a sake tsugunar da su a wasu kasashe za su so zuwa inda suka zaba. Basa son a kai su kasashen dake cikin tashin hankali
Sansanin 'yan gudun hijira na Mahama dai yana da tazarar kilomita 160 daga kan iyaka tsakanin Rwanda da Burundi kuma yana dauke da kusan 'yan gudun hijira 44,000 da yawancin su mata da yara ne.
A nata bangare, wata mace a sansanin Marie Rose Niyongere, 'yar kasar Burundin dake sansanin Mahama tayi kira ga gwamnatin kasar Rwanda da sauran kasashen Duniya da su bari su zabi inda suke so a kai su. Ta ce suna son Rwanda sabode akwai tsaro da kwanciyar hankali a gare su da Iyalin su.(Fatimah Jibril)