Ministar harkokin wajen kasar ta Rwanda Louise Mushikiwabo, ta shaidawa manema labarai cewa, taron zai samu halartar wakilai sama da 3000, ciki hadda shuwagabanni 50 na kasashe, da kusoshin gwamnatoci, da wakilan ofisoshin diflomasiyya. Zai kuma gudana tsakanin ranekun 10 zuwa 18 ga watan Yuli mai zuwa.
Mushikiwabo ta ce yanzu haka ana ci gaba da gudanar da shirye shirye a matakin karshe domin tabbatar da nasarar taron. Ta ce manyan kudurorin taron na wannan karo sun hada da zaben sabon shugaban kungiyar ta AU, da mataikakinsa, da ma wasu kwamishinonin kungiyar masu yawa.
Har ila yau, za a kaddamar da sabon Fasfo na nahiyar Afirka, wanda zai samar da damar safarar hajoji, da zirga-zirgar al'ummun nahiyar ba tare da wani tarnaki ba. (Saminu Hassan)