A bisa ga alkaluman da cibiyar kididdiga game da sha'anin iyali ta kasar Ruwanda ta fitar ya nuna cewa, kimanin kananan yara 367,810 ne ake bautar da su a kasar.
Karamar kasar wadde ke tsakiyar Afrika, ta gudanar da bikin ranar tunawa da ranar yara kanana ta Afrika shekaru 25 ke nan, wanda aka gudanar a kauyukan Gikoba da Tabagwe a gundumar Nyagatare ta lardin Gabas na kasar.
Ana gudanar da bikin ranar tunawa da yara kanana na Afrika ne a ranar 16 ga watan Yunin kowace shekara tsakanin kasashe mambobin kungiyar tarayyar Afrika.
Taken bikin na bana shi ne rikice-rikice da tashin hankali a Afrika, ba da kariya ga dukkan kananan yara.
Da take jawabi a lokacin bikin, Judith Uwizeye ministar aikin gwamnati da kwadago ta kasar Rwanda, ta ce, sam bai dace ba ga daidaikun mutane ko kungiyoyi su dinga shigar da yara kanana cikin aikace-aikace masu tsanani don hakan na tauye musu rayuwarsu.
Shi ma ministan ilmi na kasar Rwanda Dr. Papias Malimba Musafiri, ya ce wannan ranar wata babbar dama ce wajen wayar da kan jama'a game da illolin dake tattare da bautar da kananan yara.
Ana gudanar da bikin tunawa da kananan yara ne a ranar 16 ga watan Yuni, kuma an fara bikin ne tun a shekarar 1991, wanda kungiyar OAU a wancan lokacin ta kirkiro da shi. (Ahmad Fagam)