Faraministan Guinee ya jaddada niyyar gwamnatin kasar na tattaunawa tare da 'yan adawa
Firaministan kasar Guinee, Mamady Youla ya jaddada a ranar Litinin niyyar gwamnatinsa na ci gaba da yin tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki a fagen siyasa, musamman ma 'yan adawa domin kai ga cimma ra'ayi guda, da zai taimaka ga jure sabaninsu. Mamady Youla dake magana a gidan rediyon kasar, a lokacin da aka fi saurare, ya tunatar da cewa tattaunawar da aka kaddamar a baya bayan nan a karkashin kulawarsa ba a yanke ta ba. Ya bayyana a yayin wannan hira, cewa gwamnatin Guinee ta mika hannunta ga masu ruwa da tsaki a fagen siyasa domin tattaunawa, ganin cewa ba za a iya gina kasa ba tare da zanga zanga ba. Sanarwar faraministan Guinee ta fito a jajibirin wata zanga zangar 'yan adawa ta ranar Talata a Conakry, babban birnin kasar. 'Yan adawar sun samu izinin gudanar da zanga zangar a titunan birnin Conakry daga gwamnan babban birnin. Bangarorin biyu sun yi wani zaman taro a ranar Lahadi, kan matakan tsaro na wannan zanga zanga. Game da batun tattaunawar sasanta 'yan kasar Guinee, ministan kula da harkokin cikin gida, Bourema Conde, ya ba da amsa kan wata wasika ta 'yan adawa, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin na goyon baya na ganin wannan shiri an sake farfado da shi kamar yadda bangarori daban daban suke fata. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku