in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An farfado da aikin samar da lantarki ta hanyar amfani da hasken rana a Guinea
2016-06-13 11:04:22 cri
Bisa labarin da aka samu, an ce, kwanan baya, kasar Guinea ta farfado da aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da rana a yankin Kankan na kasar.

A watan Oktoba na shekarar 2015, aka fara aikin gina yankin, amma ba da dadewa ba an dakatar da wannan aiki.

Haka kuma, matakin farko na wannan aiki shi ne gina wani yankin samar da wutar lantarki ta makamashin rana mai kilowatt dubu 8, domin samar da wutar lantarki ga birnin Kankan, sa'an nan, za a habaka shi zuwa kilowatt biliyan dubu 1.2, wanda zai iya samar da wutar lantarki ga birane uku gaba daya wadanda za su hada da Mandiana, Kouroussa, Kerouane, ban da wadannan birane uku kuma, zai samar da wutar lantarki ga tsibiran Ross na kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China