Kasar Saudiya ta baiwa kasar Guinea kujeru 7200 domin zuwa aikin hajji a wurare masu tsarki a wannan shekara, a cewar wata majiya mai tushe a ranar Alhamis. Rukunin farko na maniyatan Guinea zai tashi daga birnin Conakry a ranar 17 ga watan Agusta mai zuwa, in ji wannan majiya.
Kuma kamfanin kasar Turkiya, wato Turkish Airlines, aka baiwa kwangilar jigilar mahajjatan zuwa kasa mai tsarki.
Ko wane maniyata zai biya kudin Guinea miliyan 39,8 kimanin Euro dubu hudu.
Tsakanin shekarar 2014 da shekarar 2015, Guinea ta ga an hana ta zuwa aikin hajji dalilin annobar cutar Ebola, wacce ta kassara kasar, tare da janyo mutuwar mutane fiye da dubu biyu. (Maman Ada)