A jiya Asabar, aka fara gasar wasannin Olympics a birnin Rio. Baki daya an sami lambobin zinariya 12 a jiya. A cikin gasar wasan harbe-harben bindiga na tazarar mita 10 na mata, 'yar wasan Amurka mai shekaru 19 da haihuwa, Thrasher Virginia ta lashe gasar, wato ke nan ta sami lambar zinariya ta farko ta gasar Olympics a wannan karo. 'Yan wasan kasar Sin, wato Du Li da Yi Siling sun sami matsayi na biyu da na uku a gasar.
Daga bisani, a gasar harbe harbe na tazarar mita 10 na maza, dan wasan Vietnam, Hoang Xuan Vinh ya kara yin bajinta, inda ya samu lambar zinariya ta farko a tarihin kasar, yayin da dan wasan kasar Sin Pang Wei ya sami matsayi na uku a gasar.(Fatima)