in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta zabi kyaftin na Rio Olympic
2016-07-27 09:48:37 cri

A jiya Talata gwamnatin Najeriya ta sanar da nadin 'dan wasan tsakiyar Chelsea FC kuma kaftin din Super Eagles Mikel Obi a matsayin kyaftin din da zai jagoranci tawagar 'yan wasan kasar a gasar wasannin Rio Olympic ta 2016 da za'a gudanar a kasar Brazil tun daga ranar 5 ga wata kamawa.

Ministan wasannin Solomon Dalung, wanda ya tabbatar da hakan ga kamfani dillancin labaru na Xinhua, kana ya bayyana Funke Oshonaike a matsayin mataimakiyar kaftin din.

Shi dai Mikel yana daya daga cikin 'yan wasan 3 da suka fi yawan shekaru wanda aka gayyata cikin kungiyar wasan kwallon kafan kasar.

Ita kuwa fitacciyar 'yar wasan kwallon tebur Oshonaike, wannan shi ne karo na 6 da take halartar wasannin Olympic, tun bayan da tauraronta ya fara haskawa a wasannin Atlanta na shekarar 1996.

Ministan ya ce, an zabo Mikel da Oshonaike ne sakamakon irin kwazonsu da jajurcewa wajen kishin kasa.

Dalung ya ce, ya yi amanna cewar, kokarin da mutane biyu ke da shi zai kawowa tawagar 'yan wasan na Najeriya alheri, kuma zai daga martabar kasar a idonun duniya.

Ana sa ran kungiyar 'yan wasan kwallon kafan ta Najeriya za ta tashi zuwa Rio daga Atlanta na kasar Amurka a ranar Juma'a, a inda suke samun horo. Sauran kungiyoyin 'yan wasan kasar su ma za su tashi daga Abuja a wannan rana.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China