in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi mika tutar kasa ga tawagar Nijar da zata halarci wasannin Olympic na shekarar 2016 a Rio
2016-07-30 12:18:18 cri
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya mika a ranar Jumma'a da yamma a Niamey da tutar kasa ga 'yan wasan da zasu wakilci kasar Nijar a wasannin Olympic karo na 31 na shekarar 2016 a Rio, da zasu fara daga ranar 5 zuwa 22 ga watan Augusta mai zuwa.

Mambobi biyu na tawagar Nijar zasu halarci wasan ninkaya, wasu biyun su halarci wasannin guje guje da tsalle tsalle, guda a wasan Judo da kuma wani guda a wasan Taekwondo.

Shugaban Nijar ya mika tutar kasa ga Abdoulrazak Issoufou Alfaga, da dukkan 'yan Nijar suke alfahari da shi kan wadannan wasanni. Mai rike da damara baka a ajin dan na wasan Taekwondo, a yanzu haka yana na goma sha daya bisa jerin 'yan wasan Taekwaondo na duniya kana na biyu a Afrika.

Shugaban kasa ya bukace su da kadda suyi kasa a gwiwa ga fatan kasa baki daya, musammun ma idan aka yi la'akari da kudi da kayayyaki da aka sanya musu. Tawagar Nijar zata bar Niamey a ranar Litinin domin zuwa kasar Brazil.

Nijar na halartar wasannin Olympic karo na goma sha daya. Kuma kasar ta samu lambar yabo ta tagwulla har zuwa wannan lokaci tare da dan wasan dambe Issaka Dabore a wasannin Munich na shekarar 1972. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China