in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa tutar kasar Sin a kauyen wasannin Olympics dake Rio
2016-08-04 09:59:40 cri
A jiya ne tawagar 'yan wasan kasar Sin da za su fafata a gasar wasannin Olympics a birnin Rio na kasar Brazil suka yi bikin kafa tutar kasar a tsangayer wasannin na Olympics da ke birnin Rio.

A jawabinsa yayin bikin kafa tutar wanda ya samu halartar daukacin 'yan wasan na kasar Sin, shugaban tawagar 'yan wasan kasar Sin Liu Peng ya ce, masu shirya gasar wasannin ta Rio sun shirya kasaitaccen bikin kade-kade da raye-raye gabanin bikin kafa tutar ta kasar Sin. Ya kuma bayyana fatan 'yan wasan kasar Sin za su taka rawar gani a gasar, tare da nuna kyawawan dabi'un Sinawa da karfafa fahimtar juna tsakanin sauran 'yan wasa daga sassan daban-daban na duniya.

Tawagar ta kasar Sin mai kunshe da 'yan wasa 411, za ta fafata a wasanni 210 a gasar da za a bude gobe Jumma'a, biyar ga watan Agusta.

Kamar yadda aka saba ana sa ran kasar Sin za ta lashe lambobin zinare a wasannin kwallon tebur, badminton, wasan kasada, daga kayan nauyi, harbi da kuma wasan zamiya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China