in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin IOC ya amincewa 'yan wasan kungiyar Rasha 271 su shiga gasar Rio
2016-08-05 11:23:55 cri
A jiya Alhamis ne, kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya (IOC) ya sanar da amincewa da 'yan wasan kasar Rasha 271 su shiga gasar wasannin Olympics na Rio.

A ranar 30 ga watan Yuli ne, rukunin bincike da ya hada da membobi uku na kwamitin gudanarwa na kwamitin IOC ya yanke hukunci kan 'yan wasan Rasha bi da bi, wadanda suka sami izini daga kungiyoyin wasanni daban daban na duniya. Wadannan 'yan wasa ba za su shiga gasar Olympics ta Rio ba sai har sai sun cika sabbin sharuddan da kwamitin IOC ya gindaya a kwanan baya.

Bisa wadannan sabbin sharudda, mafi yawan 'yan wasan kasar Rasha sun sami izinin shiga gasar, adadin da ya kunshi 'yan wasa 387 baki daya.

Kafofin yada labarai na kasashen yammacin duniya da dama sun zargi shawarar da kwamitin IOC ya yanke ta baiwa wasu daga 'yan wasan Rasha iznin shiga gasar Olympics ta Rio. Game da wannan batu, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta duniya Thomas Bach ya sha bayyana cewa, kamata ya yi a baiwa kowane mutum damar kare kansa.

A ranar 18 ga watan Yuli ne, hukumar yaki da kwayoyin da ke kara kuzarin 'yan wasa, ta fitar da wani rahoto mai zaman kansa cewa, hukumar kula da wasannin motsa jiki ta Rasha ta yi rufa-rufa kan 'yan wasanta game da kwayoyin kara kuzari, tare da yunkurin boye batun. A sabili da haka, ta yi kira ga kungiyar da ta haramtawa 'yan wasan Rasha shiga gasar Olympics ta Rio kwata-kwata. A yayin taronsa a ranar 24 ne kwamitin IOC ya yanke hukuncin janye haramci a kan 'yan wasan Rasha gaba daya wajen samun damar shiga gasar, wato a maimakon haka ne, za a bar kungiyoyin wasanni daban daban na duniya su yanke shawara ko za a baiwa 'yan wasan kasar iznin shiga gasar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China