Kasar Rwanda na cigaba da rike matsayi mai kyau game da yaki da cin hanci daga cikin takwarorinta na gamayyar kasashen dake gabashin Afrika. A cewar wani rahoton auna mizalin cin hanci (IPC) na shekarar 2015 na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya Transparency International, Rwanda ita ce kasa ta hudu inda cin hanci bai yi kanta ba sosai a nahiyar Afrika, kana kuma kasa ta 44 a matakin duniya.
A bangaren gamayyar kasashen dake gabashin Afrika, kasar Rwanda ita ce ta farko a gaban kasashen Tanzaniya, Kenya, Uganda da Burundi. Haka kuma, a bangaren kasashen dake kudu da hamadar Sahara, kasar Botswana ita ce kan gaba, kana kasashen Cap-Vert, Seychelles, Maurice da Namibiya na dafe mata baya. (Maman Ada)