Haka kuma, Asusun IMF ya nuna cewa, karuwar bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara a watan Afrilu, ya ragu zuwa kashi 3 bisa dari, amma yanayin karuwar tattalin arziki a ko wace kasa ya bambanta sosai.
Bugu da kari, asusun na IMF ya fidda bayani cewa, duk da kyakkyawan yanayin samun bunkasuwa a wannan fanni, amma adadin karuwar tattalin arziki ba zai kai kashi 6 bisa dari ba, kana saurin karuwar al'ummomi ya fi saurin karuwar tattalin arziki a wannan yanki, lamarin da ya kara matsa lamba ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara.
Dangane da wannan lamarin, shugaban sashen Afirka na asusun ba da lamuni na IMF ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Afirka su kyautata tsarin tattalin arzikinsu, domin samun karin hanyoyin raya tattalin arziki a yankin.
Bugu da kari, asusun na IMF yana ganin cewa, a halin yanzu, akwai kasashe da dama a wannan yanki da ke da karfin raya tattalin arzikinsu, lamarin da ya kawo kyakkyawar makoma ga bunkasuwar tattalin arziki a yankin nan da dan karamin lokaci. (Maryam)