Daga ranar 15 zuwa 17 ga wata, ministocin kudi da shugabannin bankin tsakiya na manyan kasashen duniya sun hallara a birnin Washington domin halartar taron da asusun IMF da bankin duniya suka shirya a lokacin bazara. A ranar 15 ga wata, Sin ta fidda alkaluman karuwar tattalin arzikinta a farkon watanni uku na bana, wanda ya alama mai kyau ta samun dorewa.
A yayin da yake magana da wakilinmu a jiya, Zhu Min ya bayyana cewa, shugaban bankin tsakiya na Sin Zhou Xiaochuan ya bayyana yanayin da ake ciki a fannin tattalin arziki na Sin a yayin taron. Mista Zhu ya ce, mahalarta taron sun nuna babban yabo ga kwarin gwiwar Sin na tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin dorewa, tare da farin ciki kwarai. Za su nuna goyon baya ga gwamnatin Sin wajen kara yin kwaskwarima.
Ban da haka, hukumar kididdiga ta Sin ta ba da alkaluman a ranar 15 ga wata cewa, jimillar GDP ta Sin ta karu da kashi 6.7 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, a ciki sha'anin ba da hidimomi na ci gaba da jagora, yayin da jimillar kudin da aka kashe ita ma take ci gaba da karuwa.(Fatima)