Babbar daraktar asusun bada lamuni na duniya IMF Christine Lagarde, ta ce Najeriya ba ta bukatar wani bashi a yanzu, duk kuwa da matsalar kamfar kudi da kasar ke fuskanta.
Lagarde wadda ta bayyana hakan ga manema labarai a jiya Talata, jim kadan bayan ganawarta da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar, ta kara da cewa, ziyarar da take yi a Najeriyar ba ta da nasaba da batun samar da bashi, illa dai kawai nazartar yadda za a karfafa yakin da mahukuntan kasar ke yi da cin hanci da rashawa, tare da fadada matakan inganta manufofin gudanar da mulki cikin managarcin yanayi.
Jami'ar ta ce gwamnatin kasar mai ci na aiki tukuru wajen ganin al'amuran tattalin arzikin kasar sun inganta, wanda hakan ke tabbatar da kyakkyawan fatan da ake yiwa kasar.
Yanzu haka dai Lagarde na ci gaba da gudanar da ziyarar kwanaki 4 da take yi a Najeriya.(Saminu Alhassan)