Wata sanarwa da asusun ya fitar a jiya Laraba, ta nuna cewa gyare-gyaren su ne irin su mafiya girma, da asusun ya gudanar a manufofin sa na gudanarwa, tun bayan kafuwar sa, kuma sun yi la'akari da muhimmancin da kasashe masu saurin bunkasa ke da shi a harkokin tattalin arzikin duniya.
Sanarwar ta ce kasar Sin tana matsayi na uku a jerin masu fada aji game da hannayen jarin asusun, inda take biye da Amurka da Japan, wadanda ke gaban ta a wannan fage.
Kaza lika kasashen India, da Brazil da Rasha, su ma na cikin goman farko a wannan jadawali na IMF.